Mai neman jam’iyar Republican ta tsaida shi takarar shugaban kasa Mitt Romney ya lashe zaben fidda dan takara a jihohi shida daga cikin goma da aka gudanar da zabe jiya Talata, da ya hada da karamin rinjaye da ya samu a jihar Ohio, jihar da take da muhimmanci a zaben Amurka.
Ya doke babban abokin hamayyarshi tsohon dan majalisar dattijai Rick Santorum da kashi daya bisa dari kawai. Romney ya kuma sami nasara a jihohin Vermont, da Virginia, da Massachesetts da Idaho da kuma Alaska.
Da yake jawabi a Boston, Romney ya yi harsashen cewa, zai lashe zaben fidda dan takarar ya kara da shugaba Barack Obama a zaben shugaban kasa da za a gudanar a watan Nuwamba.
Mai neman tsayawa takarar yana bukatar wakilai dubu daya da dari daya da arba’in da hudu kafin kasancewa dan takarar jam’iyar ta Republican. Kafin zaben na jihohin goma da aka gudanar jiya da ake kira Super Tuesday, Romney yana kan gaba da sauran abokan takararshi da yawan wakilai, ya kuma kyautata zaton zaben na jiya zai kara mashi karfi. Sai dai ya gaza samun goyon bayan ma’aikata da kuma ‘yan jam’iyar masu tsats-tsauran ra’ayin addini wadanda suke goyon bayan Santorum.
Santorum ya lashe zaben na jiya Talata a jihohin North Dakota da Oklahoma da kuma Tennessee da begen sake yin tashe bayan lashe zaben da ya yi a jihohi uku watan jiya.