Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Carlos Slim Na Kasar Mexico Ya Fi Kowa Arziki a Duniya


Hamshakan attajiran Amurka Bill Gates da Warren Buffet wadanda Carlos Slim ya doke a arziki a cewar kamfanin Bloomberg.
Hamshakan attajiran Amurka Bill Gates da Warren Buffet wadanda Carlos Slim ya doke a arziki a cewar kamfanin Bloomberg.

A cikin kasurguman attajiran akwai 5 daga Turai, 3 daga Asiya,2 daga yankin kudancin nahiyar Amurka, 1 kuma dan kasar Canada

Wata sabuwar kididdiga ta tantance cewa Carlos Slim, hamshakin mai harakar sadarwa na kasar Mexico, shi ne ya fi kowa arziki a duniya.

kamfanin dillancin labaran harakokin kasuwanci na Bloomberg ya fada Litinin din nan cewa sabon jerin sunayen attajiran duniya ishiri mafiya arziki ya nuna cewa Carlos Slim mai shekaru 72 ya na da kudin da su ka dara dola miliyan dubu 68.

Slim ne ya mallaki kamfanin America Movil na Mexico wanda ke daya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa na duniya. Slim ya doke hamshakan attajiran Amurka biyu wato Bill Gates mai kamfanin Microsoft da kuma Warren Buffet dan shekaru tamanin mai kamfanin Berkshire Hathaway. Kamfanin dillancin labaran harakokin kasuwancin na Bloomberg ya ce Gates na da sama da dola miliyan dubu 62, shi kuma Buffet na da kusan dola miliyan dubu 44.

Kamfanin dillancin labaran harakokin kasuwancin na Bloomberg ya ce Ingvar Kamprad na kasar Sweden mai kamfanin Ikea da kuma Bernard Arnault na kamfanin LVMH na Paris, kasar Faransa, kowannen su ya mallaki dola miliyan dubu 42.

Jerin sunayen kasurguman attajiran ya kunshi mutum biyar daga Turai, uku da Asiya, biyu daga yankin kudancin nahiyar Amurka, da kuma daya dan kasar Canada.

XS
SM
MD
LG