Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Akufo-Addo Ya Gabatar Da Jawabi Kan Yanayin Da Kasa Ke Ciki


Akufo-Addo
Akufo-Addo

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya bayyana cewa kasar ta fuskanci koma baya, amma yanzu tana kan shawo kan kalubalen. Haka kuma Shugaban ya amince da daukar alhakin matsalolin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta, a matsayinsa na shugaba mai cikakken iko. Ya bayyana hakan ne a jawabinsa ga majalisar dokoki kan Yanayin da Kasa ke Ciki (SONA) a Accra.

Yayin da yake jawabin, kamar yadda sashe na 67 na kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1992 ya tanada, shugaba Nana Akufo-Addo ya bayyana kalubalen da aka fuskanta a baya, yadda kasar ke turbar murmurewa, da kuma burin ci gaba mai dorewa, a bangarorin tattalin arziki, ilimi, noma, tsaro, lafiya, wasanni da shirin gwamnati kan babban zaben kasa mai zuwa.

Akufo-Addo and John Mahama
Akufo-Addo and John Mahama

Yace: ‘Mun yi tuntube, amma mu na kan tashi. An ji mana rauni, amma muna kan warkewa. Mun tashi da kafarmu. Mun kakkabe kurar da kanmu, kuma yanzu muna fuskantar gobe da kwarin gwiwa’. Haka kuma shugaban ya dauki alhakin kalubalen da kasar ta fuskanta.

Sai dai shugaban marasa rinjaye a majalisa, Dokta Cassiel Ato Forson, ya bayyana rashin amincewa da shugaba Akufo-Addo kan halin da kasar ke ciki. Ya ce 'yan Ghana ba su jin dadin mulkinsa domin, ‘Yanayin da kasarmu take ciki babu alamun alheri. Ba mamaki da talakawan Ghana da kwararru ke tsallakewa kasashen waje don neman arziki."

GHANA PARLIAMENT Courtesy Akufo-Addo Facebook
GHANA PARLIAMENT Courtesy Akufo-Addo Facebook

Dokta Forson ya kara da cewa, biyu cikin ‘yan Ghana uku ba su da aikin yi; lamarin da shugaban kasa yaki tabowa cikin jawabinsa. Kuma yanzu ana canjin $1 kan GHC 13, alhali a lokacin tsohon shugaban kasa John Mahama ana canjin $1 kan GHC 3.80 ne.

A tsokacinsa game da ikirarin da shugaba Akufo-Addo ya yi cewa, Ghana na farfadowa daga kalubalen da ta fuskanta, Masanin tattalin arziki, Hamza Attijjany, ya ce: ‘Maganar Shugaban gaskiya ce domin daga 2021 zuwa 23 tsadar kaya sai ta haura zuwa kashi 50 cikin 100 amma yanzu ta sauko zuwa kashi 23 cikin 100. Wannan ci gaba ne idan aka yi la’akari da alkaluma. Sai dai mutane ba za su ga ci gaban hakan ba saboda, tsadar kaya bai dacewa da samun kudadensu. Maganar da shugaban kasa ya yi, abu ne kan faifai, ba za a yi dogaro da shi ba."

Wasu ‘yan Ghana sun bayyana ra’ayinsu kan jawabin shugaban, inda Abdullah Iddrisu yace shi ba zai amince da abin da shugaban ya fada ba, domin a baya ya dau alkawura amma bai cika ba, domin haka zai dauki mataki a zabe mai zuwa.

Shi kuma Alhaji Karki a nasa bangaren ya ji dadin jawabin shugaban kan tsaro, musamman yadda za a dauki mataki a rikicin garin Bawku. Sai dai bai ji dadin rashin tabo batun rashin aikin yi da ya yi kamari a kasar ba.

‘Yan majalisar dokoki za su fara muhawara kan jawabin yanayin da kasa ke ciki yau Laraba, 28 ga watan Fabrairu 2024.

Saurari rahoton Idriss Abdullah:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG