Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Ghana Ya Bada Shawarar Yadda Za A Inganta Tattalin Arzikin Afirka


Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo
Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo

Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo, ya yi kira ga shugabanni da gwamnatocin kasashen Afirka da su hada kai, su dau matakin zuba hannun jari na kashi talatin cikin dari a cibiyoyin hada-hadar kudi na Afirka da nufin inganta ma’aunin wadannan cibiyoyi yadda za su tallafawa ci gaban Afirka.

Shugaba Akufo-Addo ya yi wannan kira ne a yayin jawabin da ya gabatar a taron shugabannin kasashe da na gwamnatocin Afirka da aka gudanar a taron shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka (AU) karo na 37.

Taron, wanda aka yi wa taken “Kafa cibiyoyin hada-hadar kudi ta Tarayyar Afirka a tsarin ajandar Afirka don sake fasalin tsarin hada-hadar kudi na duniya.”

Shugaban ya nuna cewa, a halin yanzu, dukkan kasashen Afirka suna ware kashi dari bisa dari (100%) na asusunsu na ketare ga cibiyoyin hada-hadar kudi da ke wajen Afirka, duk kuwa da cewa hakan ba ya kawo wani alfanu ga nahiyar.

Yace "dukkanmu mun yarda cewa yadda tsarin hada-hadar kudi na duniya ke aiki ba ya taimaka mana [Afirka], kuma akwai bukatar yin wasu muhimman sauye-sauye a tsarin. Amma yin hakan kuma na buƙatar mu ['yan Afirka] mu ɗauki wasu matakai da za su taimaka mana wajen samun kudaden da za su tafiyar da tattalin arzikinmu".

Shugaban ya kara da cewa, idan har aka samu hanyar kara karfin samun kudade ga cibiyoyin Afirka, to lallai an samu turbar samar da kudaden ci gaban Afirka.

Bincike da aka gudanar ya zuwa shekarar 2021, na cewa jimillar ajiyar kasashen Afirka dake kasashen waje ya kai kimanin dalar Amurka tiriliyan 1.1.

Mai sharhi kan tattalin arziki da harkokin kudi, Hamza Attijjany yace “kudaden da ake ajiyewa a wasu bankuna, musamman a Turai; daloli ne, wasu kuma Yuro, wasu ma gwal ne ake ajiyewa. A duk lokacin da kasar ta shiga matsalar karayar darajar kudi ko kuma in kasar za ta yi cinikayya da kasashen waje sai a yi amfani da wadannan kudaden.”

A cikin 'yan kwanakin nan, shugabanni da gwamnatocin kasashen Afirka sun kara kaimi wajen kafa kungiyar lamuni ta Afirka da cibiyoyin hada-hadar kudi na AU guda uku; da suka haɗa da Babban Bankin Afirka (ACB), Asusun Ba da Lamuni na Afirka (AMF), Bankin Zuba Jari na Afirka (AIB) da kirkirar kasuwar hada-hadar hannayen jari (PASE).

Malam Nuhu Eliasu, wani Malamin tattalin arziki da harkokin kudi a Jami’ar Islamiyya ta Ghana, kuma babban darektan dandalin muhawara da ba da shawarwari, waton Advocacy and Policy Alternative Forum a turance, ya yi karin bayani ga alfanun da za a samu idan aka yi aiki da shawarar.

“Idan gwamnatocin Afirka suka rike kashi 30 cikin 100 na kudaden da take ajiyewa a waje, idan gwamnatocin suna bukatar rance, za su iya zuwa su amsa ba da ruwa da yawa ba, wanda zai taimakawa gwamnatocin gudanar da ayyukan ci gaba. Haka kuma, ‘yan kasuwan Afirka za su iya zuwa su samu rance, su bunkasa kasuwancinsu. Kuma hakan zai bude ayyukan yi da kuma kawo ci gaba a Afirka.”, a cewarsa.

Daga hagu: Shugaba Akufo-Ado da Shugaba Ruto
Daga hagu: Shugaba Akufo-Ado da Shugaba Ruto

Shugaban kasar Kenya, William Ruto, a jawabinsa ya nuna goyon bayansa ga wannan shawarar da shugaba Akufo-Addo ya gabatar. Ya ce shawarar na da matukar muhimmanci idan nahiyar Afirka na son tsallakewa zuwa mataki na gaba.

Saurari rahotan Idriss Abdullah:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG