Shugaba Abd Rabbuh Mansour Hadi, da sauran jami’an gwamantinsa ne suka yi murabus.
Wannan lamari dai yazone biyo bayan kaiwa da komowar siyasa tsakanin shugaban da mayakan Houthi wadanda ke rike da kasar tun ranar Litinin.
Kakakin Gwamnatin Yemen a nan Washington, Mohammed Albasha ya bayyana cewa shugaban zaiyi murabus ta kan dandalin sada zumunta jiya Alhamis.
Wasu kalamai da Firayim Minista Khaled Bahah ya buga akan shafin Facebook, da kamfanin dillancin labaran Reuters ya rawaito, cewa gwamnatin kasar bata sha’awar shiga surkullen siyasa ne a kasar.
Da yake magana daga birnin Sanaa jiya Alhamis, wakilin MDD Jamal Benomar, ya bayyana cewa za’a kawo rigingimun siyasa ne idan kungiyoyin dake hamayya da juna suka mutunta yarjejeniyar da aka cimma dake cewa a rarraba karfin iko a kasar domin kawo karshen tashe-tashen hankula.