Wani manzon Majalisar dinkin duniya, ya ce gwamnatin Yemen ta cimma yarjajjeniyar kawo karshen yaki da 'yan tawayen Shi'a jinsin Houthi, wanda ya yi tsanani cikin 'yan kwanakin nan.
Mai bada Shawara na Musamman ga Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya, kan Al'amarin Yemen, Jamal Benomar, ya fadi jiya Asabar cewa yarjajjeniyar za ta yi shinfida ga hadin kan kasa da kwanciyar hankali. Ya ce an cimma yarjajjeniyar ce bayan tuntubar dukkannin bangarorin sosai don a warware rikicin.
Benomar ya yi maganar ce jim kadan bayan wani kwamitin tsaro da kwamnati ta kafa, ya kafa dokar hana fita a wasu sassan Sana'a, babban birnin kasar, inda 'yan Houthi din su ka ce sun kwace gidan talabijin din gwamnati. Shaidu sun ce sassan ginin na ci da wuta yayin da wasu mutane ke makale ciki, wadanda su ka jijji raunuka.
Kwana guda kafin nan, an hallaka mutane sama da 40 a wasu tashe-tashen hankula, yayin da wasu 'yan bindiga su ka kwace wasu wuraren da 'yan sanda da sojojin kan yi sintiri a Sana'a. A ranar Jumma'a kuma, jiragen saman kasa da kasa sun dakatar da sauka birnin.