Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Reshen Alka'ida Ya Hallaka Ba-Amurke Luke Somers


Luke Somers, dan jarida mai daukar hoto
Luke Somers, dan jarida mai daukar hoto

Kungiyar al-Ka'ida ta reshen kasashen Larabawa ta hallaka ba-Amurken dan jarida mai daukar hoton nan Luke Somers wanda ta yi barazanar hallaka shi a 'yan kwanakin nan.

Wani ba-Amurken dan jarida mai daukar hoto ma kafar labarai da wani malamanin makaranta dan Afirka Ta Kudu, sun mutu a wani yinkurin da Amurka ta jagoranta na ceto su a kasar Yemen a jiya Asabar.

Sakataren Tsaron Amurka Chuck Hagel ya fadi jiya Asabar cewa, dan jarida mai daukar hoton mai suna Luke Somers da malamin makarantan mai suna Pierre Korkie din, wadanda su ke tsare da su ne su ka kashe su, wato 'yan kungiyar ta'addar al-Qaida a kasashen Larabawa, a yayin wani kokarin kubutar da su da sojojin Amurka da na Yemen su ka yi a lardin Shabwa da ke kudancin kasar. An yi garkuwa da mutane biyun na tsawon sama da shekara guda.

Hagel ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan Somers da Korkie.

Hagel ya ce an hallaka 'yan ta'adda da dama a yayin yinkurin ceto mutane, matakin da ya ce an dauka ne saboda bayanai sun nuna cewa ran Somers na cikin matukar hadari.

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi tir da abin da ya kira "kisan kai na rashin imani" da "'yan ta'addan al-Qaida su ka yi." Ya ce shi ya ba da umurnin a ceto Somers da sauran wadanda aka yi garkuwa da su a wuri guda a ranar Jumma'a.

Hagel ya ce Somers, dan shekaru 33 da haihuwa ya fuskanci barazanar kisa tun ranar Alhamis.

Sakataren Tsaron ya jinjina ma wadanda su ka yi yinkurin ceton, ya na mai cewa an aiwatar yadda ya kamata.

An hakkake cewa kungiyar al-Qaida da masu alaka da ita, na samun dinbin miliyoyin dala kowace shekara, daga kudin fansar mutanen da su kan yi garkuwa da su, kuma ta yi Allah wadai da yawan kashe mutanen da kishiyarta, wato kungiyar Daular Islama, kan yi garkuwa da su.

XS
SM
MD
LG