Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirye-shiryen Sassauta Dokar Hana Zirga-zirga A Amurka


Gwamnatin shugaba Donald Trump na ci gaba da shirye-shiryen ganin jihohi sun sassauta dokar hana zirga-zirga, da bude wasu bangarorin tattalin arzikin kasar, a yayin da kuma take fama da yaduwar cutar coronavirus a cikin ma’aikatan fadar shugaban kasa ta White House.

Akalla ma’aikatan fadar 2 ne aka same su da cutar ta COVID-19, daya mai kula da shigar shugaban kasa ne, daya kuwa sakatariyar watsa labarai ta mataimakin shugaban kasa Mike Pence.

Mai Magana da yawun mataimakin shugaban kasar ya ce, an yi gwaji ga matamakin shugaban kasa an kuma tabbatar ba ya dauke da cutar, kuma a yau Litinin zai dawo bakin aiki a fadar White House, inda ake sa ran zai yi wata ganawa ta hanyar sadarwar bidiyo da wasu gwamnonin jihohi akan annobar ta coronacirus, da kuma tattalin arziki.

"Mataimakin shugaban kasar zai ci gaba da bin shawarwarin jami’an lafiya na fadar ta White House, amma ba zai killace kan sa ba", a cewar Devin O’Malley a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi.

Mutane fiye da miliyan 1 da dubu 300 ne suka kamu da cutar ta coronvirus a kasar Amurka, inda fiye da 80,000 suka rigamu gidan gaskiya.

A Jihar New York da annobar ta fi kamari, an sami mace-mace na fiye da mutum 27,000, ana kuma sa ran sake bude al’ammura a jihar nan da zuwa ranar Juma’a, kamar a sauran jihohi da aka sami karancin yaduwar cutar, da su ma za su bude al’ammura.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG