Shugaban Amurka Donald Trump ya ki amincewa da matsayar da majalisar dokokin kasar ta yi na dakatar da shi daga yin amfani da karfin soja a kan kasar Iran har sai ya sami amincewar majalisar.
A cikin wani sako da ke bayana kin amincewar ta shi, Trump ya kira kudurin a zaman "cin fuska", kana ya ce, kudurin zai yi kawo tarnaki ga karfin ikon shugaban kasa na kare Amurka da kawayenta.
'Yan majalisar sun goyi bayan kudurin a lokacin da ake ci gaba da ta da jijiyar wuya tsakanin Amurka da Iran, inda su ka bayyana bukatarsu na tabbatar da karfin ikon ayyana yaki a hannun majalisar dokoki.
Shugaba Trump ya ba da umarnin kai wani hari a watan Janairu da ya hallaka baboon jami'in sojan Iran, Janar Qaseem Soleimani. Kwanaki kadan Iran ta mayar da martani tare da kai hari da makamai masu linzami a kan sojojin Amurka da ke Iraqi, da ya haifarwa sama da sojojin Amurka 100 cutar kwakwalwa.
Ma’aikatar tsaron Amurka ta fada a farkon makonnan cewa ta baiwa dakarun kasar 29 lambar yabo ta "Purple Heart" da ta ke baiwa wadanda aka kashe ko aka jikkata a lokacin yaki.
Facebook Forum