Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Sauya Fasalin Kudin Najeriya Ya Janyo Ce-Ce-Ku-Ce Tsakanin Wasu Kungiyoyi Da Manazarta


Naira
Naira

Batun sauya fasalin kudin Najeriya da babban bankin kasar ya ce zai yi yana ta janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin kungiyoyi masu zaman kansu da ma manazarta a harkokin kudi, musamman ma akan lokacin da bankin na CBN ya bayar.

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya ce kwanaki 45 ne kacal ya diba wa kasa na kamalla cajin kuma shugaban kasa Mohammadu Buhari ya amince da haka.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele

Wannan batu na sauya fasalin manyan kudin Najeriya, na Naira 200, 500 da kuma Naira 1000 daya da babban bankin Najeriya ya ce zai yi tun daga ranar 15 ga watan Disamba na bana zuwa 31 ga watan Janairun badi ya dauki hankalin kungiyoyi masu zaman kansu irin su Miyetti Allah Kautal Hore inda shuagabansu na kasa Abdullahi Badejo, ya ce ya kamata mahukunta su kara tsawon lokacin da za a yi canjin kudaden.

A cewar Badejo, yawancin mutane da ke kauyuka ba su da bankuna, kuma suna da kudi musamman ma Fulani makiyaya.

Badejo ya ce a halin yanzu ba a riga an wayar da kawunan mutanensa ba, kuma yawancin su ba su da labarin canja kudin, saboda haka akwai jan aiki a gaba.

Shi kuwa shugaban kungiyar CISLAC kuma jami'i a Transparency International a Najeriya Auwal Musa Rafsanjani ya ce gaba daya ma, sauya fasalin kudin ba shi da wani amfani a kasar yanzu.

CBN
CBN

Rafsanjani ya ce kungiyar sa ta yi nazari akan sauya fasalin Naira kuma sun ga cewa ba zai kawo wani gyara a tattalin arzikin Najeriya ba.

Amma ga mai nazari a tattalin arziki Yusha'u Aliyu, yana ganin sauyin fasalin kudin ya zo a daidai kan lokaci.

Yusha'u ya ce yin sauyin zai farfado da tattalin arzikin kasa kuma ya zo daidai da lokacin da ‘yan kasa ke bukukuwa na karshen shekara, ko kuma debo amfanin gona, kuma zai sa a samu karin ayyukan yi, amma Yusha'u ya ce, akwai bukatar a fahimtar da mutane da yarukan da suka sani.

Fadar shugaban kasa ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya amince da a sauya takardun kudin a cikin kwanaki 45, daga 15 ga watan Disamba na wannan Shekara zuwa 31 ga watan Janairu na shekara 2023.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Shirin Sauya Fasalin Kudin Najeriya Ya Janyo Ce-Ce-Ku-Ce Tsakanin Wasu Kungiyoyi Da Manazarta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

XS
SM
MD
LG