Matasan da aka dauka tuni aka kammala basu horo a kan aikin duba gari da na tabbatar da tsaftace muhalli a manayan biranen jihar. Sama da nera miliyan dari aka kebe domin horar da matsan da kuma biyansu albashi.
Alhaji Hassan Nuhu, shugaban shirin ya ce nan gaba za'a kara daukan matasa dubu daya wadanda z'a hora da su domin su yi aiki a asibitoci dake kananan hukumomi da yanzu suke fama da karancin ma'aikata. Wasu daga cikin matasan da aka dauka sun yi godiya da farin ciki cewa sun samu ayyukan yi karkashin shirin cire tallafin man fetur da ake kira "SURE-P".
Samarda aikin yi ga matasa wata hanya ce ta inganta da tabbatar da tsaro a kasar. Kamar dai yadda aka sani kungiyoyin 'yan ta'ada kan yi anfani da matasa marasa aikin yi. Idan an samar masu da aikin yi ba zasu shiga yin ta'adanci ba.
Ga karin bayani daga Mustafa Nasiru Batsari.