Da yake tabbatar da haka ga wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Maiduguri, kakakin rundunar ta JTF, Leftana-Kanar Sagir Musa, yace an damke shugaban na jam'iyyar ANPP kwanaki hudu zuwa biyar da suka shige.
A bisa dukkan alamu, an kama shi ne jim kadan a bayan da matasa 'yan banga dake farautar 'yan Boko Haram a Maiduguri, suka kai farmaki a kan gidan jami'in suka banka masa wuta.
Kanar Sagir, ya kuma gaskata labarin cewa dakaru sun killace Unguwar Bulabulin Nganeram a Cikin Maiduguri, inda ake gudanar da abinda ya kira "yaki da ta'addancin da ya mamaye wannan unguwa."
Yace sun samu makamai da yawa, sun kuma kashe ko sun kama 'yan Boko Haram masu yawa cikin wannan unguwa.
Kwanakin baya aka yi ta jin labarin cewa 'ya'yan Boko Haram sun sulale suka mamaye wannan unguwa, a bayan da ko dai suka kori mazauna unguwar karfi da yaji, ko kuma su mazauna unguwar suka gudu daga gidajensu da kawunansu a bayan da 'yan bindigar suka fara shiga su na zama cikin wannan unguwa.
Sojojin su na bi gida-gida cikin wannan unguwa, su na farautar makamai da 'yan bindigar da suka boye su. An ce har yanzu ana gwabzawa a tsakanin su jami'an tsaro na rundunar JTF da wadannan 'yan bindiga dake kokarin sajewa da jama'a.
Haka kuma, sojojin sun ce sun gano, kuma su na kira ga jama'a da su yi hattara sosai da 'yan bindigar da suke shiga su yi lullubi kamar mata domin su sulale ko kuma su je aikata wani mummunan aikin a wani wuri.
Ga cikakken bayani a tattaunawar Haruna Dauda da Kanar Sagir Musa: