WASHINGTON, DC —
Mutane talatin da biyar ne suka mutu a garuruwan Bama da Malam Fatori a karamar hukumar Kukawa a jahar Borno. Kakakin rundunar jami'an tsaron hadin guiwa a jahar Borno, JTF, Laftana-Kanal Sagir Musa ya tabbatarwa manema labarai afkuwar wannan al'amari a ciki wani sakon imel da ya tura mu su. Kakakin ya ce 'yan Boko Haram ake zargi da kai hari kan ofishin 'yan sandan kwantar da tarzoma a garin Bama, wadanda jami'an tsaron JTF su ka kaiwa dauki. Harin yayi sanadiyar mutuwar dan sanda daya a yayin da rundunar ta harbe maharan goma sha bakwai har lahira, sojoji biyu kuma sun raunata. Laftana Kanal Sagir Musa ya ce baicin harin na Bama, haka kuma wadanda ake zargin cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai harin kan jami'an tsaron kan iyaka a garin Malam Fatori, a can ma sun kashe sojoji biyu, ita kuma rundunar jami'an tsaron ta kashe 'yan kungiyar goma sha biyar. Laftana-Kanal Sagir Musa ya yi karin haske a tattaunawar su da Haruna Dauda Biu, wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a jahar Borno:
Kakakin rundunar jami'an tsaron hadin guiwa , JTF, Laftana-Kanal Sagir Musa ya tabbatar da sahihancin labarin