Abokin aiki Bello Galadanci ya zanta da masani kan harkokin siyasa da na yau da kullum Dr. Usman Bugaje. A firarsu Dr. Bugaje ya ce wannan dambarwa da ake ciki wadda ta kai fiye da wata biyu, dambarwa ce wadda da wuya a ce an samu masalaha yadda ake so saboda fitinar da aka tsokano ba'a san inda zata kare ba. Abu na biyu shi ne wadanda suka yiwa shugaba Morsi juyin milki da Amurka ta ki ta ce juyin milki aka yi basu yi zaton masu goyon bayan Morsi zasu fito su yi dafifi kamar yadda suka yi ba, basu kuma yi zaton cewa akidarsu tsatsaurar akida ce. Ya ce mutanen duniya gaba daya suna ganin Kasar Masar ta kama hanyar kasar Syriya saboda an cusa ra'ayin addini da kabilanci da rarrabuwan kawunan mutane cikin kasar.
Lamarin da kasar ke ciki yanzu babu wanda ya san mokomarta. Ita kanta Amurka bata da wata masaniya sabili da haka sun tura su John McCain da wasu. Bayan abubuwan da suka gani da irin tattaunawar da suka yi su John McCain suma kansu sun ce juyin milki a ka yi wanda ya samu asali daga sojojin da suka ki Morsi suka kuma yi borin tubeshi. Juyin milkin bai samu asali daga jama'ar kasar ba. Sojoji ne suka yi anfani da rahotannin siri dake cewa wai Morsi bashi da goyon bayan manyan kasashen Larabawa da ma Turawan milkin mallaka. Don haka da wuya a ce ga makomar kasar Masar a yanzu.
Su kansu sojojin sun gaji da dagewar magoya bayan Morsi. Suna barazanar kawar dasu da karfi da yaji da goyon bayan kasashen yammacin turai. Idan ko sojoji suka yi masu korar kare yayin da su suna ganin hakinsu a ka tauye to babu wanda ya san yadda za'a kare.
Da alamu cewa dimokradiyar da Amurka da kasashen turai suka mara ma baya ya dore kodama bai anfani mutanensu ba. Wanda kuma basu goya ma baya ba da wuya ya dore ko kuma ya samu karbuwa a wurinsu kamar kasar Venezuela
Ga cikkaken bayani.