Yayin da kasashen Yammacin Turai suka ki fitowa kara su kira abun da sojojin kasar suka yi a matsayin juyin mulki sai gashi kasar Saudiya da wasu a nahiyar Larabawa suna taya sojojin murna da ma sabbin shugabannin da sojojin suka nada.
A cikin kasar Masar mutane da yawa sun dauki lamarin juyin mulki duk da kin amincewa da hakan na kasashen yammacin turai. Wanda aka zanta da shi ya ce idan an ce shugaba Musulmi ne sai aga shugabannin kasashen duniya sun yi masa taron dangi domin ba Musulunci suke so ba.Da Aliyu ya jawo hankalinsa bisa ga matsayin kasashen Musulmai kamar su Saudiya sai ya hakan ya faru ne sabo da tsananin furofaganda na tsafofin shugabannin kasar kan 'yan uwa Muslmai da suka yi shekara da shekaru suna yi a kafofin labarai kamar jaridu da radiyo da telebijan da dai sauransu. Domin haka suka zauna suka yi nazari kan hanyoyin da zasu bi kana suka soma aikawa da labarai da rahotanni zuwa jakadun kasashe cewa shi Morsi baya jin magana. Amma sabanin abubuwan da suka ce shi Morsi ya kira duk jam'iyyu ya bayyana masu abubuwan dake gudana. Sai dai kila domin kin addinin Musulunci sai suka juya masa baya.
Ga karin bayani a wannan rahoton.