Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Wai Abubakar Shekau Ne Kuwa


Irin aikin ta'adancin Boko Haram
Irin aikin ta'adancin Boko Haram

A wani sakon bidiyo wani mai magana ya ce shi ne Abubakar Shekau amma da walakin

Yau kusan wata biyu ke nan da sojojin Najeriya dake fafitika da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi ikirarin mutuwar shugaban kungiyar Abubakar Shekau sanadiyar wani hari da suka ce sun kai a sansanin da kungiyar ta ja daga.

To kwatsam sai ga wani bidiyo inda wani yake ikirarin shi ne Abubakar Shekau. Amma matsalar ita ce bidiyon murya ce kawai babu hoton da ya nuna yana magana domin a samu a kwatanta da wadan da ya yi da can kafin a ce ya mutu. An san cewa idan Shekau da aka sani yana magana ana ganinsa a bidiyon to amma ba a wannan da ya shigo hannunmu ba.

A cikin bidiyon ya ambato sunayen shugabannin duniya da zasu ji kunya. To amma abun mamaki ya ambaci sunan Mrs Thatcher wadda tuni Allah ya yi mata rasuwa a cikin wadanda zasu ji kunya domin shi yana nan da ransa. Da alama da walakin cikin wannan sabon ikirarin

Ga karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG