A wata hirar da yayi da VOA Hausa, Muhammadu Marwana, yace idan Abubakar Shekau yana so, zasu ci gaba da yin tafiya da shi, amma a matsayin mujahidi ba na Imam ba. Ya ce wata "cibiyar dake gudanar da harkokin Musulunci ta duniya" ce ta aiwatar da shi.
Babu wata majiya ta dabam, ko kuma mai zaman kanta, wadda ta tabbatar da sahihancin ikirarin da shi Muhammadu Marwana yake yi.
Ga hirar da yayi da VOA Hausa kan wannan batun...
MARWANA: To Alhamdulillahi yanzu ragama dai na amshe ta, kamar yadda aka umurce ni. Na amshe ta a kan tafiya ta Mujahidai. Babu kuma sauran wani abu wanda ya shafi, ehm na tashin-tashina, na abinda ya shafi mu ya mun mu. Shi Abubakar Shekau yanzu idan ya biyo mu zamu yi tafiya da shi, amma a matsayin mujahidi yake, ba a matsayin shi na Imam Abubakar Shekau ba.
VOA: To wannan sauyi daga ina ne aka samu?
MARWANA: Eh, babbar cibiyarmu ce wadda take gudanar da harkokin Musulunci ta duniya. Alhamdulillahi wannan daga shugabanninmu ne, mu kanmu ba kashin kanmu ba ne. Kuma Alhamdulillahi bisa ga shawarar da na kawo kuma suka hawo kan shawarar, suka dauke ta suka yarda da ita a matsayina na memba nasu na Afirka ta Yamma, ba ma na Arewa kadai ba. Suka dora ni ga wannan nauyi, kuma na dauka.
VOA: To yanzu shi Abubakar Shekau yana ina?
MARWANA: Abubakar Shekau yana nan, ya zauna..ai ba zan sanar da kai wai ga inda Abubakar yake ba. Yana nan..duk da rade-radi da wasu suka fito suka ce muku a’a ya mutu, an kashe shi ko ba ya nan. Abubakar (Shekau) bai fi awa uku ko hudu da nayi magana da shi ba. Sai dai mutuwa ba ta kadan, sai dai in a daidai wannan lokaci da muke magana da kai ya mutu ko wani abu. Amma a dai lokutan da aka ce ga shi (wani abu ya same shi) Abubakar yana raye. Ban jima ma da yin magana da shi ba.