Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Me Sake Fasalin Tsarin Najeriya Ke Nufi?


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da Mataimakinsa
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da Mataimakinsa

Karuwar masu neman a raba Najeriya ya sa an soma kiran a sake fasalin tsarin mulkin Najeriya domin a samu zaman lafiya ko da yake kawunan 'yan kasar bai zo daya ba kan wannan batun.

Dr. Abubakar Umar Kari masanin kimiyar siyasa na Jami'ar Abuja ya bayyanawa Muryar Amurka ma'anar sake fasalin tsarin mulki Najeriya.

Dr. Kari ya ce sake fasalin mulkin kasa na nufin duk wani arziki dake wani yankin kasar bai kamata ya zama na kasar gaba daya ba, na wannan yankin ne.

"Abun da yankin ko lardin zai yi shi ne ya dinga biyan gwamnatin tarayya haraji na abun da ya samu. Kowa ya ci gashin kansa." In ji.

Sai dai 'yan siyasa irinsu Alhaji Aliyu Sale Bagare wanda tsohon mataimakin gwamna ne a jihar Yobe suna da ra'ayi daban, ya ce tsarin da kasar ke kai yanzu baya bukatar wani garambawul.

Yana mai cewa duk wanda yake son a sake tsarin mulkin Najeriya ya isa a kirashi "babban maci amana amanar kasa" domin bai san irin gwagwarmayar da shugabannin farko suka yi ba kafin kasar ta samu 'yanci daga turawan mulkin mallaka.

Ya ci gaba da cewa Allah ne kadai ya san dalilin da ya sa ya dunkule kasar ta zama kasa daya kana ya albarkace ta da mutane da dimbin arzikin mai da ma wasu.

Domin jin cikakken rahoto kan wannan batu, saurari wakilinmu Hassana Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG