Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga da Jami'an Tsaro Sun Fafata a Garin Misau


Gwamnan jihar Bauchi Isa Yuguda
Gwamnan jihar Bauchi Isa Yuguda

Daren Laraba mazauna garin Misau a jihar Bauchi sun kwana cikin tsoro da firgita sanadiyar hare-harbe na bindigogi da kuma tada bamabamai.

Wasu 'yan bindiga sun farma garin Misau daren Laraba inda suka tayin lugudan wuta babu gaggautawa kafin jami'an tsaro su cimmasu.

Wani mazaunin garin yayi bayanin abun da ya gudana a cikin daren. Yace da misalin karfe goma sha biyu aka fara jin aman bindiga mai karfin gaske. Karar bindiga da fashewar bamabamai sun bazu koina a garin kuma babu wanda bai ji ba. Mutane sun rude basu san daga wane sashin garin karan ke fitowa ba. Yace kowa dake cikin garin a rude yake. Baya cikin hankalinsa.

Da yammacin Talata an lura da shigowar wasu cikin motoci uku da mutane sanye da kayan soji. Haka ma aka ga babura sun zo sun wuce. Mai bada bayanin yace mutane da yawa sun gansu hatta mutanen dake komawa kayuka sun ci karo da su.

Yace akwai musayar wuta tsakanin 'yan bindingan da jami'an tsaro. Yace sun samu bayanin cewa sojoji sun samu sukunin wargaza maharan. Sojojin sun kame motoci biyu na maharan. Sun cafke wasu kana wasu sun jefar da makamansu sun shiga daji.

Yanzau harbe-harben ya lafa. Garin ya samu dan natsuwa. Amma da yake mutane sun firgita suna ganin maharan suna nan sun boye ne. An samu shawo kan lamarin domin jami'an tsaro sun yi abun da yakamata kuma cikin dan lokaci.

A wata sabuwa kuma wasu 'yan bindiga sun yi fashin motoci biyu. Daya ta Majalisar Dinkin Duniya ce. Ta biyun kuma mallakar gidan telibijan jihar Bauchi ce. Kakakin 'yan sandan jihar Bauchi DSP Haruna Mohammed yace ranar Laraba da yamma wasu 'yan bindiga suka kwace motoci.

Ga rahoton Abdulwahab Mohammed.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:29 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG