Kamar yadda gwamnan yayi bayani kawo yanzu dai an ansamo guda goma sha hudu. Hudu sun diro ne daga motar yayin da ake tafiya dasu. Guda goma kuma sun kubuta wani Lawani ya gansu ya kaisu wurin hukuma.
Gwamnan yace an bude takardar ragista inda iyaye zasu rubuta sunayensu da na 'ya'yansu da basu gani ba. Iyaye hamsin sun riga sun yi ragista ko. Gwamnan yace yayi magana da shugaban makarantar da kuma hakinmin garin Chibok. Shi kanshi gwamnan yana shirin zuwa garin na Chibok domin ya gani menene zasu iya yi.
Dangane da kokarin da gwamnati ke yi na gano yaran gwamnan yace bai cancanta ya bayyana abun da su keyi a bainar jama'a ba. Yace dole a yabi jami'an tsaro domin kokakrin da suke yi. Yace a dinga tayasu da addu'a. Babban abun da ya fi damunsa shi ne samun yaran lafiya ba tare da cin mutuncinsu ba.
Gwamnan yace babu wani addini Musulunci da Kiristanci da ya yadda a sace yara a yi masu fyade. Yace jahilci ne kadai zai ba mutum irin wannan zarafin.
Ga rahoton Haruna Dauda Biyu.