Sanata Ahmed Lawan yace sam ba zasu amince da sake sabunta dokar ta baci ba a jihohin nan uku na arewa maso gabas. Yayin da yake magana gabanin karewar wa'adi na biyu na dokar a karshen wannan makon lokacin da zata cika shekara daya yace ya zama wajibi a dakatar da dokar haka nan, a dauki wata sabuwar dabara. Kin sabunta dokar bai nuna za'a janye sojoji da sauran jami'an tsaro ba. Idan ma shugaban kasa na bukatar karin sojoji yana iya yin hakan.
Yace ya kamata a duba kudurin da mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro wato Kanal Sambo Dasuki ya bayar ne cewa a duba a kawo wasu abubuwa na cigaba yadda jama'a ba zasu dinga goyon bayan 'yan ta'ada ba.
Abu na uku shi ne a sasanta amma ba tare da yin anfani da kwamitin Turaki ba domin kwatin din na amshin shata ne. Abun da shugaban kasa yake so shi zasu gaya masa. Su kuma 'yan kungiyar ba zasu yadda da irin wannan kwamitin ba. Ya ba gwamnati zabi. Ko ta cire Turaki ta sa wani wanda bashi da alaka da gwamnati ko kuma ta rushe kwamitin ta nada wani sabo da zai kunshi mutanen da basa cikin gwamnati.
To saidai 'yan PDP daga jihohin uku da yanzu su ne 'yan adawa suna goyon bayan sabunta dokar. Ado Buniyadi daya daga cikin shugabannin PDP a Yobe yace idan an rage tsaro zasu bubugesu. Yace ina Boko Haram? An kama 'yan Boko Haram sun fi dari to amma ina gidan iyayensu? Shi Ahmed Lawan da yace kada a sabunta dokar bashi da gida a Yobe ko kasa.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.