Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SHARHIN AMURKA: Bala’in Yunwar Da ‘Dan Adam Ya Haddasa A Sudan


Sudan June 22, 2024.
Sudan June 22, 2024.

Daga cikin rabe-raben matsalar karancin abinci, kaso na 5, wanda shine matsananciyar yunwa, yafi tsanani.

Tsarin karkasa rabe-raben karancin abinci, IPC, ya bayyana yanayin da matsanancin rashin abinci ko muhimman kayayyakin bukata na rayuwa duk da daukan matakan jurewa hakan, inda yunwa da talauci da tsananin rashin abinci mai gina jiki suka bayyana karara.

Idan har kaso 20 na al’umma na fama da matsananciyar yunwa, sannan idan mutum 2 daga cikin mutane 10, 000 dake rayuwa a wuri suna mutuwa a kowace rana, toh ana ayyana cewar gaba-dayan yankin yana fama da matsananciyar yunwa.

Wannan shine halin da ake ciki yau a kasar Sudan, a cewar sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya.

“Kasar Sudan na fama da daya daga cikin mafi girman rikicin bil adama da bai takaita ga yau kawai ba, harma da rayuwar gaba-daya,” a cewar jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield.

“Akalla yankuna 5 na fama da matsalar matsananciyar yunwa a halin yanzu. Muna hasashen samun karuwar hakan a wasu yankunan 5, nan da watanni masu zuwa. Kuma akalla yankuna 17 ne ke cikin hatsarin afkawa wannan irin yanayi a wannan dan tsakani. Fiye da mutane 500, 000 ne, ciki harda kananan yara, ke fadi tashin ganin sun rayu.”

Wannan bala’i “sakamako ne na kai tsaye na kazamin yakin da aka shafe watanni 20 ana gwabzawa,” a cewar jakada Thomas-Greenfield. Bugu da kari, hukumomin sudan sun dakatar da hadin gwiwa da ipc, dake karkasa rabe-rabe karancin abinci,” tare da kawo cikas ga kokarin kasashen duniya na samarda tallafin jin kai da kuma magance yunwa.”

Kowace daga cikin mambobin dake zaune anan a yau ya ga hujjar dake tabbatar da cewar dukkanin bangarorin dake rikici da juna a sudan saf da rsf sun aikata laifuffukan yaki. Kowace daga cikin mambobin dake zaune a anan a yau ya ga shaidar dake tabbatar da cewar rsf ta aikata laifuffuka akan jinsin bil dama kuma ta aiwatar da kisan kare dangi.

Amma duk da hakan, rasha ta zabi tayi karan tsaye: inda ta zama ware sakamakon zabin data yi na jefa rayuwar farar hula cikin hatsari, yayin da take daukar nauyin bangarori 2 dake rikici da juna. eh, nace: dukkanin bangarorin 2.”

Sai dai duk da hakan, zamu cigaba da aiki ba tare da gajiyawa ba domin magance cin zarafi tare da hukunta wadanda keda hannu a hakan,” inji jakada Thomas-Greenfield.

"Duk da haka, za mu ci gaba da yin aiki tukuru don hana cin zarafi da kuma hukunta masu laifi," in ji Ambasada Thomas-Greenfield.

“Amurka ta kakaba taakunkumai a matsayin martani akan laifuffukan da aka aikata da kuma cinikin makamai, a shirye muke mu dauki karin matakai nan bada jimawa ba. yanzu, muna jaddada kiranmu na daukar matakin bai daya, muna bukatar kawayenmu suyi tarayya damu wajen kakaba takunkumai akan mutane da kungiyoyin da ayyukansu suka ta’azzara wannan rikici.”

“Muna kira ga dukkanin masu hannu a rikicin su kawo karshen laifuffukan da suke aikatawa,” a cewar jakada Thomas-Greenfield,” domin kawo karshen rikicin, tare da gaggauta kyale shigar kayan agaji ba tare da gindaya wani sharadi ba domin milyoyin mutane su samu abinci da ruwan sha da muhalli da magungunan da suke tsananin bukata.”

Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG