Mujallar nan ta kungiyar likitocin Amurka ta bada rahoto jiya talata cewa matakan da aka dauka na kayyade yadda ake sayarda taba sigari a Amurka tun shekarar 1964 sun taimaka wajen kara tsawon shekarun da ake sa ran ‘yan shekaru 40 da wani abu yanzu haka a nan Amurka zasu yi a duniya.
Amma kungiyar likitocin ta Amurka ta ce tilas a ci gaba da kokarin da ake yi domin rage yawan mutanen dake mutuwa a sanadin shan taba sigari a kasar nan.
Rahoton da babban likitan Amurka Luther Terry ya bayar a shekarar 1964, wanda a karon farko ya bayyana cewa sigari yana haddasa cutar sankarar huhu, ya girgiza Amurka sosai a lokacin da kashi 40 cikin 100 na Amurkawa su na shan taba sigari. A yau, kashi 18 cikin 100 na amurkawa ne kawai suke shan taba sigari.
Rahoton nasa ya sa an dauki matakai kamar na rubuta gargadin illolin taba a jikin kwalayensa tare da haramta yin tallar taba sigari a gidajen rediyo da telebijin a duk Amurka.
Amma kuma duk da haka, har yanzu kimanin Amurkawa dubu 443 suke mutuwa kowace shekara a sanadin shan taba sigari, kuma yana daya daga cikin manyan abubuwan dake haddasa cutar sankarar huhu, da ciwon zuciya da shanyewar jiki.