Ana sa ran cewa zuwa gobe alhamis, yanayi zai koma kamar yadda aka saba gani a irin wannan lokaci na shekara a jihohin da suke tsakiyar Amurka, yayin da a nan yankin gabashin Amurka za a ga yanayi maras tsananin sanyi kamar na lokacin da tsirai suke toho ya zuwa karshen mako.
A wani lokaci a jiya talata, dukkan jihohi guda 50 na Amurka sun ga sanyin da mizaninsa ya fi tsananin wanda ke sa ruwa ya daskare ya zamo kankara. Har a Jihar Hawaii inda ba kasafai ake yin sanyi ba, jiya sai da aka ga sanyi mai tsananin digiri 6 a kasa da mizanin daskarewar ruwa a kan duwatsun jihar.
Sanyin da ya rutsa manyan biranen yankin tsakiyar Amurka kamar Chicago da Minneapolis, ya bazu zuwa nan gabashin Amurka jiya talata. A nan birnin Washington da wasu birane na gabashi kamar NY da Philadelphia da Boston, an ga sanyi na awu 10 kasa da mizanin daskarewar ruwa ya zamo kankara. Iska mai karfi da aka fuskanta ma ta sa jikin mutum yana jin sanyin ya fi haka tsanani.
A jihohin da suke kudu, inda ba kasafai ake yin sanyi ba, an ga sanyin da wadannan jihohi ba su taba ganin irinsa ba.
Wannan sanyi mai tsanani ya sa an rufe makarantu, da birkita zirga zirgar jiragen kasa, ya kuma sa aka soke tashin dubban jiragen sama. An bayarda rahoton mutuwar mutane akalla biyar a sanadin wannan sanyi a nan Amurka.