'Yan Niger 678 dake birnin Bangui babban birnin Afirka Ta Tsakiya gwamnatin ta Niger ta dawo da su gida sakamakon rikicin addini da na kabilanci da ya barke a kasar wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka a kasar. Tun da rigingimun suka barke 'yan kasar ta Niger suka makale a Afirka Ta Tsakiya. 'Yan kasar Niger din sun shiga wani hali na tagaryara.
'Yan Niger din sun sauka a filin saukan jiragen sama dake Niyamey inda aka tarbesu. Wadanda suka iso sun hada da mata da maza da matasa da yara. Jami'an agaji sun cigaba da kulawa da su.
Wasu da suka iso sun fadi irin abubuwan da suka gani.Wata Hadiza Garba ta ce sun fita cikin wani mugun halin da basu taba gani ba. Sun ga yadda aka kama samari aka yanka wuyansu. Mata ma da suke da ciki sai a tsaga cikinsu a fitar da jariran a yanka. Dare da rana kowa na gudu. Wani abun da ya sa suka sake shiga cikin mawuyacin hali shi ne rashin jakadar da kasarsu bata da a Afirka ta Tsakiya.
Su ma maza sun fadi abubuwan da suka gani. Alhaji Dauda Gidankaro ya ce a shekaru 60 da ya yi a duniya bai taba ganin inda ya ga ana datse mutum kamar itace ba. Ya ce duk wanda yake garin Bangui babu mai kwanciyar hankali. Kowa na zaune ba barci ba hutawa. Ya ce a gabansa ya taka gawarwaki sun fi dari.
Malama Sa'adatu Malam Barmo ita ce shugabar kwamitin da gwamnatin kasar ta kafa musamman domin mutanen da aka dawo dasu gida. Ta ce gwamnati ta tanadi a kai kowa har garinsa ko kauyensa. Duk abun da zasu ci su sha da inda zasu kwana gwamnati ce ta dauki nauyin yin hakan. Duk abubuwan da suke bukata cikin gaggawa an tanadesu.
Ga rahoto.