Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Serah Luka Daliba Ta Biyu Da Aka Ceto Daga Sambisa


Serah Luka Daya Daga Cikin Yan Matan Chibok Da Aka Ceto.
Serah Luka Daya Daga Cikin Yan Matan Chibok Da Aka Ceto.

Dakarun Najeriya sun ce sun sake kubutar da wata daga cikin daliban makarantar Chibok da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su fiye da shekaru biyu da suka gabata.

Kakakin rundunar sojin Najeriya, Kanar Sanu Usman Kuka Sheka, ya fada a wata sanarwa da ya fitar cewa, sunan yarinyar Miss Serah Luka, kuma ta fito ne daga garin Madagali da ke jihar Adamawa.

Rundunar sojin Najeriyar har ila yau ta fitar da hoton yarinyar, sanye da wani dogon hijabi mai launin shudi da aka saba sakawa a yankin, wanda kuma aka ga sauran ‘yan matan Chibok sun saka a hoton bidiyon da aka fitar a baya.

Wannan yarinya ita ce ta biyu cikin daliban Chibok 219 da aka kubutar bayan da aka sace su a shekarar 2014.

A ranar Talatar da ta gabata ne aka ceto Amina Ali, mai shekaru 19 tare da jaririyarta bayan da ‘yan kato da gora suka kai wani samame a dajin Sambisa da ke jihar Borno.

A jiya ne Amina da mahaifiyarta suka gana da shugaba Muhammadu Buhari a Fadarsa da ke Abuja, inda ya jaddada cewa gwamnatinsa, na iya bakin kokarinta domin ganin a kubutar da sauran ‘yan matan.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG