Tawagar gwamnan Borno ta isa Abuja jiya inda gwamnan ya gabatarda Amina Ali wa shugaban kasa Muhammad Buhari.
Ita dai Amina Ali tana cikin daliban makarantar 'yan mata da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace daren goma sha hudu ga watan Afirilun shekarar 2014 yayinda suke shirin rubuta jarabawar sauke karatun sakandare a garin Chibok.
Gwamnan ya shaidawa shugaban kasa cewa jajircewar yarinyar, dauriya da jimrewa suka sa ta rayu har ta kai lokacin da Allah ya sa aka kubutar da ita.
'Yan Boko Haram sun yiwa Amina auren dole har ma ta haifi yarinya jaririya wadda take rike da ita a hannun.
Da murna tare da yiwa Allah godiya da sojojin kasar Shugaba Buhari ya marabci Amina, diyarta, mahaifiyarta, gwamnan Borno da sauran jami'an tsaro da na gwamnati. Shugaba Buhari ya jadda cewa gwamnatinsa ba zata amince da auren dole ba.
Ga karin bayani