Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Sanar da Kara Kubuto Wata 'Yar Makarantar Chibok


Amina Ali dalibar farko da sojoji suka kubutar
Amina Ali dalibar farko da sojoji suka kubutar

Wata sanarwa daga hedkwarae rundunar sojin Najeriya tace sun kara kwato wata 'yar makarantar Chibok

Sanarwar mai dauke da sa hannun kakakinta Kanar Sani Usman Kukasheka tace dakarun bataliya ta 331 tare da soji masu kwance bamabamai da hadin gwuiwar 'yan kato da gora na Buratai sun kubutar da wasu mutane da dama.

Dakarun sun yi sintiri ne a kauyukan Shettima Abo, Hong da Balabili daga karamar hukumar Damboan jihar Borno inda suka fafata da 'yan Boko Haram. Sun samu sun kashe 'yan ta'adan kimanin talatin da biyar.

Dakarun sun kuma kubutar da mata da yara tasa'in da bakwai wadanda 'yan Boko Haram suka sace.

Cikin matan da aka kubutar har da karin wata dalibar makarantar Chibok mai suna Sarah Luka wadda take lamba 107 na jerin daliban da kungiyar Boko Haram ta sace fiye da shekaru biyu da suka gabata.

Dalibar tana samun kiwon lafiya a barikin soja dake garin Biu.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:55 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG