Hukumar kwallon kafar Najeriya ta NFF ta hana da sayar da ‘yan wasan na kungiyar matasa masu kasa da shekaru 23 da na kasa da shekaru 17, ga kungiyoyin kwallon kafa na Turai ba tare da bin tsarin da ya kamata ba.
Ministan matasa da wasanni na Najeriya Barista Solomon Dalung ne ya fadi haka jiya a Abuja, bayan da ya sami labarin hukumar NFF na sayar da ‘yan wasa ba bisa tsarin da yakamata ba. yayi gargadin bayar da takardar canjin ‘dan wasa ba tare da an tabbatar cewa ‘dan wasa ya amince ba.
Ya ci gaba da cewa wannan abin mamaki ne ace matasan da suka yiwa Najeriya rawar gani wajen lashe kofin zakarun nahiyar Afirka a Senegal da lashe kofin gasar matasa ‘yan kasa da shekaru 17 na hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ace ana sayar da ‘yan wasan ba tare da sanin su ba, kuma basu fahimci irin kwantiragin da suke rattaba hannu ba.
Solomon Dalung dai ya sha alwashin ‘daukar mataki ga duk wanda aka samu yana bayar da takardar canjin ‘dan wasa ba tare da anbi doka ba, kuma yace ba zai rufe idanunsa ba idan har aka ci gaba da mayar da matasan bayi.