Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, Karl-Heinz Rummenigge, yace kulob din ta jima da sanin cewa kwach din ta, Pep Guardiola, zai bar kulob din a karshen wannan kakar kwallon kafa.
Rummenigge yace tun a karshen watan Satumba ya fara jin kishin-kishin din wannan batun, amma “sai suka ba kwach din lokaci domin ya yanke shawarar inda ya dosa cikin tsanaki, ba su tinkare shi ba.
Shugaban na Bayern Munich ya fadawa jaridar Bild cewa a lokacin liyafar kirsimeti da suka gudanar makonni biyu da suka shige, “Guardiola ya same ni yace yana son rungumar wani kalubalen dabam, kamar ma yana neman gafara ta cewa yana son barin kulob din.Ni dai rai na bai baci da shi ba.”
A ranar lahadin da ta shige Guardiola, mai shekaru 44 da haihuwa, ya nufi kasarsa Spain domin hutun kirsimeti, ya bar Bayern din ta sanar da duniya cewa ba zai sabunta kwantarakinsa na shekaru 3 ba.
Carlo Ancelotti, mai shekaru 56, shi zai gaji Guardiola a Bayern Munich a yayin da ake rade-radin cewa Guardiola zai koma Manchester City.
Rummenigge yace ya san inda tsohon kwach din nasa zai dosa, amma kuma zai bari shi da kansa Guardiola da kuma kungiyar da zata dauke shi su bayarda sanarwar hakan.
Game da sabon kwach din da zai horar da ‘yan wasan Bayern Munich, Rummenigge yace yana da kwarin guiwa sosai domin “Carlo Ancelotti ya samu nasara a duk inda ya zauna. Ya lashe kofin zakarun kulob kulob na Turai har sau uku.” Yace ba karamar sa’a suka ci ba da suka kamo tsohon kwach din na Real Madrid domin kusan rabin kulob-kulob na Turai sun yi zawarcinsa.