Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Babu Kwach Kamar Jose Mourinho A Duk Duniya


Wakilin Jose Mourinho, yace har yanzu, babu wani kwach ko manajan da ya kai Mourinho a duk fadin duniya, duk da korarsa da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi ran alhamis.

Mourinho dan kasar Portugal ya bar Chelsea a karo na biyu a bayan da shugabannin kulob din suka yanke shawarar cewa kakar kwallon bana ba ta yi dadi ba, domin maki daya kawai ya raba kungiyar da fadawa cikin wadanda za a kora daga Firimiya Lig a karshen shekara.

Wakilin na Mourinho, Jorge Mendes, ya fadawa wata jaridar Portugal mai suna A Bola cewa, “Babu wani abinda ya sauya a game da Jose Mourinho. Shi din ne dai. Kuma duk da abinda ya faru a Chelsea, har yanzu babu wani kwach ko mai koyar da kwallon kafa a duniya da ya kamo shi.”

Ya ci gaba da cewa, “A lokacin da Mourinho ya bar Chelsea a karon farko, ya rungumi kalubale, ya kuma yi abubuwan da babu wanda yayi imanin cewa zai iya yi a lokacin, watau ya karbi ragamar koyar da kungiyar Inter Milan ya jagorance ta ta lashe Kofin Zakarun kulob kulob na Turai, da wasannin lig-lig na Serie A na Italiya, da kuma Coppa Italiya, nasarar da babu kamar ta.”

Mendes yace daga nan, “Mourinho ya je shi kungiyar Real Madrid, ya jagorance ta ga samun nasara ta tarihi a wasannin lig-lig na Spain, ta kawar da duk wani abin tarihin da kungiyar FC Barcelona ta taba yi a lokacin, sannan kuma ta lashe kofin Copa del Rey.”

Kungiyar Chelsea dai ta ce zata maye gurbin Mourinho na dan wani lokaci da Guuus Hiddink dan shekaru 69 da haihuwa kuma dan kasar Netherlands, wanda a shekarar 2009 ya taba zama manajan wucin gadi na kungiyar ta Chelsea.

XS
SM
MD
LG