Mai kulob din Chelsea ta kasar Ingila, Roman Abramovich, ya kori manajan nasa dan kasar Portugal a saboda yadda kungiyar ta kasa yin abin kirki a bana.
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta raba gari da manajanta Jose Mourinho, a bayan da aka shafe makonni ana rade-radi game da makomarsa a kulob din.
Kungiyar Chelsea, wadda it ace ke rike da kofin Firimiya Lig, ta sha kashi a hannun Leicester City a karo na biyar cikin wasannin Firimiya Lig guda 7 na karshe da ta buga, inda har Mourinho y ace ‘yan wasansa sun sayar da shi.
Duk da yake Chelsea ta kammala wasannin zagayen farko na gasar Cin Kofin zakarun Kulob Kulob na Turai a zaman ta daya a rukuninta bayan da ta doke Porto da ci 2-1 a makon da ya shige, kashin da ta sha a hannun ‘yan wasan Leicester City ya bar ta a lamba ta 16 a teburin Lig ta Firimiya, watau dab da rukunin wadanda za a cire daga wasannin idan suka kammala a haka.
Wata sanarwar da Chelsea ta bayar ta ce “Dukkanmu a nan Chelsea muna godiya ga Jose a saboda gagarumar gudumawar da ya bayar tun komowarsa kulob din a zaman manaja a 2013.”
“Kofunan Firimiya Lig 3 da ya lashe, da Kofin Kalubale na FA, da kofin Community Shield, da kofunan Lig 3 a lokuta biyun da yayi yana zaman manajanmu, sun sa babu wani manajan Chelsea da ya taba samun nasara irin tasa a cikin shekaru 110 da kafa kulob din. Amma kuma Jose da hukumar gudanarwa sun yarda dukkansu cewa sakamakon wasanninmu a wannan shekarar bai yi kyau ba, kuma kowa yayi imanin cewa zai fi kyau a gare mu baki daya, kowa ya kama hanyarsa.”
Har yanzu dai Chelsea ba ta bayyana wanda zai gaji Mourinho ba.