Shirin ya biyo bayan wasu batutuwa da sauye-sauyen alkibla da ya auku tsakanin manyan jami’iyyu da suka shiga zaben cike gurbi na Majalisar Wakilai na yankin Jos ta Arewa da Bassa, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben, duk da cewar APC ce ke mulki a kananan hukumomin biyu, da jahar da kuma tarayya.
Wani kusa a jami’iyyar APC a Jos ta Arewa, Alhaji Jamilu Baba ya ce bai yi mamakin rashin cin zabe da APC ta yi ba, saboda shugabannin jami’iyyar ne suka nemi tursasa wa mutane su zabi dan takarar da ba su san shi ba.
Shi ma wani kusa a jami’iyyar PDP da ta lashe zaben, Bitrus Kaze ya ce abin da ya auku a zaben shi ne damokradiyya ta yadda mutane suka sami damar zaben dan takarar da suke so.
‘Dan takarar jami’iyyar PRP da ya zo na biyu a zaben, Adamu Muhammad Alkali, ya yi barazanar shiga kotu.
Alhaji Ali Promoter, wani mai fada aji a Jos ta Arewa, ya ce abin takaici ne yadda aka sami cece kuce tsakanin al’ummar Jos da gwamnati da suka yi yarjejeniyar samun zaman lafiya.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: