A ranar Laraba ne aka rantsar da Damiba a matsayin shugaba na wuccin gadi na tsawon shekaru uku, bayan da ya jagoranci tawagar hafsoshi wajen hambarar da Kabore a watan Janairu.
Sabuwar gwamnatin mai ministoci 25 ta hada da ministan tsaro Janar Barthelemy Simpore, wanda ya ci gaba da rike mukamin da ya rike a karkashin Kabore, a cewar sanarwar umurnin.
A ranar Alhamis ne aka sanar da nadin masanin tattalin arziki Albert Ouedraogo a matsayin Firaministan wuccin gadi na kasar.
Juyin mulkin sojan Burkina Faso shi ne karo na hudu a yammacin Afirka cikin watanni 18, bayan da yi biyu a Mali da kuma daya a Guinea.
Yanzu haka sabbin hukumomin za su yi kokarin shawo kan munanan hare-haren masu kishin IS da suka mamaye yankunan kasar Burkina Faso wanda hakan ya haifar da nawaya ga albarkatun kasa kalilan da kasar ke da su.
~ REUTERS