Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar sojan Nigeria ta kashe yan kungiyar Boko Haram 27


Wani soja cikin motar yaki a birnin Maiduguri, Nigeria.
Wani soja cikin motar yaki a birnin Maiduguri, Nigeria.

Rundunar sojan Nigeria tace ta kashe mutane ashiri da tara wadanda ake zaton yan kungiyar Boko Haram ne a sumamen data fara kaiwa tun ranar Alhamis.

Rundunar sojan Nigeria tace ta kashe mutane ashiri da tara wadanda ake zaton yan kungiyar Boko Haram ne a sumamen data fara kaiwa tun ranar Alhamis.

Mai magana da yawu soja Kanal Mohammed dole yace a ranar juma'a da dare sojoji suka kashe yan tawaye ashirin a sumamen da suka kai garin Bita dake kusa da kan iyakar Nigeria da kasar Kamaru. Yace an kashe soja guda daya.

Kanal Dole yace yan kungiyar Boko Haram suna amfani da yankin a zaman inda suke kaddamar da hare hare akan kauyuka da mutane da suke bi ta yankin a motocinsu.
A ranar Juma'a rundunar soja tace an kashe yan kungiyar Boko Haram guda tara a musayar harbe harbe a arewa maso gabashin Nigeria.

Jami'ai sunce a ranar Alhamis aka yi fafatwar a wani wuri dake tazarar kilomita tamani da biyar kudu da birnin Maiduguri jihar Borno babar tungar yan Boko Haram.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG