WASHINGTON, DC —
Wani shaihin malamin addinin Islama mai wa'azi, yace babban abinda zai kara tabbatar da harsashin zaman lafiya a yankin arewacin Najeriya, shi ne bunkasa ilmi ta hanyar bude makarantu, har ma da na yaki da jahilci, tare da koyawa matasa sana'a ta yadda ba zasu ji kwadayin wata fitina ba.
Sheikh Ahmad Sunusi Gumbi, yace tilas ne al'ummar arewa su san cewa Arewa fa ta kowa da kowa ne ba ta kabila ko addini daya ba, don haka ya kamata shugabanni, na siyasa da na addini, da kungiyoyi su rika shiga cikin al'umma su na fadakar da su, cikin harsunansu, game da muhimmancin zaman tare kamar yadda aka yi a baya ba tare da tashin hankali ba.
Malamin yace idan da gaske ana son aza harsashi mai karfi na wanzar da zaman lafiya, to tilas a samar da ilmi, mai yawa da kuma inganci, yana mai cewa, “...makarantu sun lalace, to ina ne zamu samu ci gaba? Ayi kokari a raya makarantu, a karantar da matasa, a karantar da yara don sune shugabanninmu a nan gaba.... A yi kokari a raya wadannan don mu samu zaman lafiya.”
Sheikh Sunusi Ahmad Gumbi, yayi wannan bayanin ne a cikin shirin wanzar da zaman lafiya a arewacin Najeriya na VOA Hausa.