To sai dai bangaren Buhari dan Shehu Usmanu Dan Fodio basu amince da cire Malam Buhari Huseini ba daga mukamin na Sarkin Yamman Badau. Dalili ke nan da 'ya'yan Buharin suka garzaya kotu inda suka gurfanar da Majalisar Sarkin Musulmi da ma gwamnatin jihar.
A zaman farko da kotun ta yi a Bodinga domin sauraren karar lauyan bangaren masu karar Rotimi Ogunnesu ya ce suna kalubalantar nadin Ibarhim Buda Badau a matsayin Sarkin Yamman Badau wadda daya ce daga bangaren gidan Buhari dake mulkin yankin. Haka kuma sun ce Ibrahim Buda ba dan gidan Buhari ba ne kuma bai gaji sarauta ba abun da lauyan ya ce ya saba ma sashe na uku na dokokin nadawa da cire sarakuna na jihar Sokoto.
Masu kara na ganin Ibrahim Buda bai cancanci sarautar da aka bashi ba domin hakan ya sabawa al'adun jama'a dalilin da suka garzaya kotu ke nan su dakatar da nadinsa. Suna kuma bukatar kotun ta tantance ko matakin da gwamnatin Sokoto ta dauka ya yi daidai ko a'a.
Amma lauya Musa Usman Ibrahim dake kare wadanda ake kara ya bayyana cewa gwamnatin jihar Sokoto ta kirkiro gundumar Badau ne ba domin zuri'ar gidan Buhari ba domin ba shi ne ya kafa garin Badau ba ko gundumar a tarihi. Lauyan ya ce wanda aka ba sarautar ya cancanta saboda wasu dalilai. Ya ce an yanke gunduma to wanene ya yanke wanene ya nada sarautar?Gwamnati ce ta yanke ta kuma nada sarauta. Domin haka ta yi daidai. Ya ce idan an yanka Wurno ko Isa ko Raba ko Silami duk na 'ya'yan Shehu ne su Bello, Rufai da Atiku kuma babu dokar da ta ce sai daga cikinsu za'a zabo sarkin yankin da aka yanka.
Ga karin bayani.