Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sana’ar Tace Sauti Da Hotan Bidiyo


Shakuol, 20, a genocide orphan at his editing studio as he talks to clients while he edits a wedding video, Giporoso, Kigali, Rwanda, Nov 20, 2013. (Hamada Elrasam for VOA)
Shakuol, 20, a genocide orphan at his editing studio as he talks to clients while he edits a wedding video, Giporoso, Kigali, Rwanda, Nov 20, 2013. (Hamada Elrasam for VOA)

A cikin shirin mu na matasa masu sana’ar dogaro da kai, wakiliyar Dandali ta zanta da wani matashi mai suna Mansur Musa Alasan, ‘dalibi a jami’ar Maiduguri kuma mai sana’ar yin aditin wato tace hotunan bidiyo da kuma wakokin hausa.

Masur ya ‘dauki shekaru biyar zuwa shida yana wannan sana’ar ta aditin, wanda suka hada da tace wakokin hausa har ma da fina finan hausa, ya kuma shiga wannan sana’a ne a dalilin sha’awar yin mu’amula da masu yin sana’ar fina finai, hakan ya tsunduma shi cikin sha’awar ‘daukar hotan bidiyo na fina finai amma dake ‘daukar hotan bidiyo ba ita bace hanyar samun abincin sa ba, ya dawo tace sauti da hotan bidiyo.

Matashin dai bai shiga makaranta don koyon sana’ar tace sauti da hotan bidiyo ba, ya dai fara koyon sana’ar tun yana karami wanda sha’awar hawa kamfuta da suke tare da abokan sa ya zamanto sanadiyar koyon ilimin aditin, daga baya kuma ya samu ubangidan da ya kara taimaka masa wajen kwarewa.

XS
SM
MD
LG