WASHINGTON, DC —
Tom Cleverley na Manchester United na son zama a kungiyar kwallon kafa na Aston Villa dan wasan gaba dai yazo Aston Villa, a matsa aro ne.
Dan shekaru ashiri da biyar da haihuwa Cleverley, ya tamakawa Aston Villa fita daga hadarin kumawa rukuni na baya.
Yace yana jin dadin buga tamaula a kungiyar ta Aston Villa, yana mai cewa idan har dama ta samu zai sake rataba hanu domin kasancewa a kungiyar ta Aston Villa.
Ya kara da cewa yana matukar farin cikin buga kwallo a kungiyar tare da abokan wasan sa domin kowane lokaci yana cikin dariya da anashiwa.
Koda yake yace sai yaga tayin da kungiyar zata yi masa tukuna amma a cewarsa buga kwallo cikin walwala da jin dadin shine kan gaba kuma hakan ya tabata a kungiyar Aston Villa.