Yayin da Manchester United da Liverpool suke kokarin samun gurbin shiga gasar zakarun kulob kulob na Turai, tana yiyuwa kungiyar Crystal Palace ta yi tasiri sosai wajan tantance ko wacece acikin su zata iya hayewa.
Crystal Palace dai ta kudiri aniyar yima Manchester United fatan kafar angulu wajan shiga wannan gasar ta zakarun kulob kulob na Turai idan sassan biyu sun gana gobe Asabar , to amma James Makaka yace wasan bana neman zuba ma garin Manchester United tsakuwa bane.
Yaran na Alan Pardew sun ja baya a cikin ‘yan makwannin nan inda suka yi asarar wasanni har guda uku a bayan da suka lashe wasanni hudu a jere a can baya.
Kungiyar Manchester United wadda ta sami kwarin gwiwa daga labarin da ya fito a tsakiyar mako cewa dan wasan PSV Memphis Depay zai doshi Old Traffort a kakar kwallo mai zuwa, tana gaban Liverpool da maki hudu to amma kuma ta yi asarar wasanni uku a jere.
Kungiyar Crystal Palace wadda take lamba ta 12 da maki 42 zata iya taka rawa akan ko wacce kungiya ce zata kasance ta 4, domin bayan krawar da zasuyi da Manchester United a wannan makon, zasuyi tattaki zuwa gidan ‘yan Liverpool sati mai zuwa domin gwabzawa da su.
Makaka ya fada wa shafin kulob din sun a Crystal Palace cewa, wannan mawuyacin wasa ne sosai amma kuma muna son irin wannan wasanni.
Daga karshe ya ce muna shi’awar wasannin da bawani matsin lamba a kanka, wato zaka iya zuwa ko Stamford Bridge ko Manchester zata zo maka gida ko kuma zaka je ma ‘yan Liverpool ba tare da wani fargaba a zuciyar kaba.