Yayinda aka kammala zabe a Najeriya, kusan kowa ya zuba ido ya ga irin rawar da gwamnati mai hawa zata taka. To ko menene abu na gaba ga matasa ganin sune ginshikin cigaba a kasar? Wannan itace tambayar da Yusuf Aliyu Harande yayi wa Alh. Aliyu Musa "Santurakin Maru".
Aliyu Musa, yace bai kamata a ce matasa sun yi dogaro ga gwamnati ba dungurungum, saboda gwamnati na iyakacin kokarinta wajen ilimantar da su, “ya kamata matasa su kara inganta kokarin da gwamnati ke yi don a sami cigaba a kasa”.
“Akwai hanyoyi da yawa da matasa zasu yi wa kansu”, a cewar Malam Aliyu. Ya kara da bada missali da wata kungiya mai zamna kanta a jihar Zamfara dake fadakar da matasa yadda zasu yi amfani da hanyar yanar gizo su tallata kayansu (ta sanya hoton a yanar gizo) tunda yanzu har wadanda basu yi ilimi ba suna amfani da yanar gizon. Wannan cigaban na daya daga cikin aubuwan da suka sa aka yi nasara a zaben bana inji Malam Aliyu.
Malam aliyu ya kuma ce yanzu kasuwanci ya tashi daga kasa kaya a kasuwa ko a shago, daga cikin dakin ka ma sai ka sayar da hajarka, ba ma a Najeriya kadai ba harma a kasashen duniya.