Matsalar zaman kashe wando tsakanin ‘yan Najeriya ya kara fitowa fili, a daidai lokacin da babban bankin duniya ya fito da rahoton da ya yi nuni da cewa, matsalar na kara ta’azara ne fiye da yadda aka saba gani a tarihi karkashin gwamnatin da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta lamarin da ya kai ga kaso 33 da digo 3 a zango na hudu a shekarar 2020.
Rahoton na babban bankin duniya dai ya yi nuni da cewa, kari da ake samu a ‘yan Najeriya da ke neman mafaka a kasashen da suka ci gaba a duniya ba ya rasa nasaba da matsin tattalin arzikin da kasar ke ciki, inda fitacciyar marubuciyar Aljannar duniya kuma ‘yar gwagwarmayar nemawa mata yanci, Malama Hafsah Abdulwahid Ahmed ta alakanta matsalar da rashin aikin yi.
Duk kokarin jin ta bakin gwamnatin Najeriya kan rahoton babban bankin duniyan da ma mafita ga matsalar zaman kashe wando da ke kara ta’azara ya ci tura.
Alkaluman rahoton na watan Yuni dai ya yi nuni da cewa, idan ba’a dauki matakan da suka dace ba, Najeriya za ta fuskanci koma baya a fannin ci gaba da ta samu na tsawon shekara 10.
Idan ana iya tunawa a cikin watan Yuli da mu ke ciki shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga matasan kasar a wani shirin gidan talabijan na Arise da su zamo masu kyawawan dabi’u don jawo hankulan masu zuba jari cikin kasar.
Kazalika shuagban kasar a jerin sakonnin da ya yi ta fitar wa a lokutan bukukuwan Sallah, ya yi kira ga 'yan Najeriya muamman matasa da su rungumi sana'ar noma don samun abin dogaro.
Saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulrauf: