Idan aka yi la’akari da duk masu kudin birnin New York masu taimakon talakawa, za’a ga cewar mutun daya ne wanda ya taba bada kyautar kudi na fitar hankali tashi daya, dalar Amurka milliyan shida wanda jama'a su kai ta mamaki.
Amma sai ga wata mata da ta bar wasiyyar cewar duk ilahirin dukiyar da ta mallaka ta ba wata makaranta don daukar nauyin ‘ya'yan marasa karfi, ita dai Sylvia Bloom, wadda ta mutu tana da shekaru casa’in da shida, ta kwashe tsawon shekaru sittin da bakwai tana aiki a matsayin sakatariya a wani ofishin lauyoyi.
Babu wanda ya taba sanin cewar ta mallaki wadannan makudan kudi, domin kuwa har danginta basu da masaniya, bayan ta mutu lauyanta ya shaida ma danginta abin da ta bari na dukiya, sai suka ce “Wannan ba gaskiya bane” sai ya bayyana yadda ta tara wannan dukiya.
A duk lokacin da babban lauya a ofishin da take aiki zai sayi hannun jari na kamfani, itama sai ta saya koda kuwa dan kadan ne, na dai-dai matsayinta na sakatariya, ta kwashe shekaru sittin da bakwai tana wannan ajiyar.
Ta mutu ta bar gidaje guda uku da bankuna goma sha daya da aka kiyasta kudin su sunkai kimanin dalar Amurka milliyan tara, dai-dai da naira billiyan uku da milliyan dari biyu da arba’in. A cikin wasiyyar ta, ta umurci da a tallafama ‘ya'yan talakawa su iya zuwa makaranta don zama wani abu a rayuwar su.
An bayyana dabi’u irin na Ms. Sylvia, a matsayin halli da ya kamata masu kudi su yi koyi da shi musamman na taimakon marasa karfi, da kuma kokarin ganin matasa sun ci gajiyar duk wani abu da mutun ya tara don ciyar da kasa gaba baki daya.
Facebook Forum