Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren PDP a Jihar Neja ya Lakadawa Wani Ma'aikaci Kashi


Gwamnan Jihar Neja Dr. Babangida Aliyu kuma dan PDP
Gwamnan Jihar Neja Dr. Babangida Aliyu kuma dan PDP

Ma'aikacin kwalajin kimiya dake Minna jihar Neja ya sha dan karen duka a hannun sakataren PDP

Wani maigadi a kwalajin kimiya da fasaha mallakar gwamnatin jihar Neja dake garin Minna ya sha kashi a hannun sakataren jam'iyyar PDP na jihar Neja.

Makarantar kwalajin kimiya da fasaha ta gwamnatin Neja da ke garin Minna babban birnin jihar ta yi allawadai da dan karen dukan da ta ce sakataren jam'iyyar PDP na jihar Neja Alhaji Aminu Yusuf ya yiwa daya daga cikin ma'aikatanta. Ko makon da ya gabata an yiwa daya daga cikin malamanta kisan gilla. Shi sakataren ya ce tabbas ya mari daya daga cikin masu gadin kwalajin sabo da rashin kunyar da ya yi masa.

Malam Adamu Aliyu Zakari shi ne shugaban ma'aikatan kwalajin ya bayyana abun da ya faru da kuma irin matakan da suka dauka. Ya ce lamarin ya faru ne domin suna son su fita daga kwalajin ta hanyar da bata kamata ba. Shi maigadin ya bayyana masu hanyar da ya kamata su bi su fita amma sakataren ya ce baisan mutuncin mutane ba sai ya mammareshi kana ya sa tawagarsa ta lakada masa dan karen kashi. Wajen mutane goma sha shida dake cikin motar safa dake bin sakataren suka farma maigadin. Shugaban ma'aikatan ya ce ba zasu yi shiru ba sai duniya ta ji kuma an yi adalci.

Gwamnatin jihar Neja ta ce kawo yanzu bata samu labarin aukuwar wannan abun kunyar ba a hukumance. Kwamishanan ilimi mai zurfi na jihar Dr Bashir Abdullahi ya ce zai bincika ya tabbatar an yi adalci da zarar ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa Bauchi. Shi sakataren na PDP ya tabbatar da marin ma'aikacin amma ba dukan tsiya ba kamar yadda ake yayatawa.

Barrister Danlami Wushishi a ma'aikatar shari'a ya ce sam bai kamata ya yi hukunci da kansa ba. Kamata ya yi ya kai maganar gaban hukuma. Bashi da hurumin marin wani koma mari daya ne. Kuma marin ma taka doka ne.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG