Sai dai kafin fara ragistan wasu 'yan jam'iyyar sun fice suna zargin wai ba za'a yi masu adalci ba.A wasu jihohi kuma ana samun gwagwarmaya tsakanin 'yan jam'iyyar na asali da wadanda suka canza sheka daga wasu jam'iyyu.
Nuhu Ribadu dake kan gaba wajen yankar katin jam'iyyar ya nuna bin lamura jikin jimiri da natsuwa shi ne mafi a'ala ga 'yan APC. Ya ce yau aka fara ragista amma wasu sun fice suna zargin ba za'a yi masu adalci ba alhali kuwa basu san abun da Allah zai basu a jama'iyyar ba. Idan mutum ya fita bisa ga kuskure ba abun kunya ba ne ya sake dawowa. Yau suna da jihohi 16 amma a wasu jihohi biyu ko uku ana samun rashin jituwa kadan kadan. Duk irin wannan ba abun mamaki ba ne. Ya ce mutane kara shiga jam'iyyarsu su keyi ko a jihar Adamawa ma.
Yayin da APC ta soma yin ragista shi kuma tsohon dan siyasa Tanko Yakasai ya kaddamar da sabuwar kungiyar dattawan arewa da nufin hada kawunan duk 'yan arewa a kowace jam'iyya domin samar ma yankin mafita. Isa Tafida na cikin bunkasa kungiyar inda ya ce kowace jihar arewa sun nemi mutane goma. Ya ce kana zasu zauna su fitar da tsarin da zasu yi aiki da shi. Zasu yi kokari su sanarda gwamnonin arewa cewa kwamitin gwamnonin arewa bai isa ba sai an hada da mutanen da ake mulka. Makasudin abun da suka sa gaba shi ne Musulmi da Kiristan arewa su fahimci juna.