Jama’a a Agadas dai sun bayyana damuwa dangane da halin da ake ciki a arewacin Nijar inda suka ce lamarin ya yi kamari sosai kuma ya kamata gwamnati ta dauki mataki.
Hukumomi a jihar Agadas dai sun koka kan yadda ake samun yawaitar sace-sace da ayyukan miyagun makamai da ke ci gaba da zame musu manyan kalubale da ke ci musu tuwo a kwarya inda suka bayyana irin matakan da ya dace a dauka domin kawo karshen wannan matsalar.
Abdourahmane Tourawa, magajin garin Agadas ya ce ana yawan samun matsoli batagari da ke tare-taren hanya kuma tushen haka na da alaka da yanayin yadda jihar Agadez cibiya ce da ke tsakanin kasashen Arewa da Kudu, da Sahara, don haka ana yawan samun baki da ke shigowa.
Mafi yawan masu aikata wannan aika aika matasa ne saboda haka kungiyoyin farar hula su ka yi kira ga hukumomi da su sama wa matasa abin dogaro da kai Lawal Taher dan kungiyar farar hula ne a Agadas.
Su ma a nasu bangare, hukumomi a jihar Agadas, kira su ka yi ga al’umma da su ba jami’an tsaro gudunmawa da ta dace domin kawo karshen matsalar dama kame duk wani mutun bata gari.
Masana sha’anin tsaro na ganin ya zama dole hukumomi su shirya wani zama na masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro don gabatar da shawarwari kan yadda za a shawo kan wannan matsala.
Saurari rahoton Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna