Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Manhaja Zata Taimaka Wajen Ilmantar Da Kowa Ba Sai A Makaranta Ba


Wai kuwa yara da basu taba zuwa makaranta ba, na iya koyar da kansu yadda ake rubutu da karatu, daga kawai sun samu na’urar kwamfuta? Tambayar da wata kungiya mai yunkurin ilmantar da duniya tayi ke nan.

Kungiyar ‘Global Learning XPRIZE’ ta ware makudan kudade da suka kai kimanin dallar Amurka milliyan goma sha biyar $15M, don cinma wannan burin. Daya daga cikin daraktocin kungiyar Mr. Matt Keller, ya ce wannan kamar abu ne mai wuyar yuwuwa ne.

Kana shawarar na iya zama kamar hauka, domin kuwa ance yaro ya koyar da kansa da kansa, daga amfani da kwamfuta, an dai bama kungiyar kwantirakin fitowa da wata sabuwar manhaja da yara wadanda basu samu damar zuwa makaranta ba, zasu iya amfani da ita wajen koyar da kansu da kansu.

A kididdigar tsangayar lissafi ta hukumar kula da kayan tarihi ta majalisar dinkin duniya UNESCO, ta tabbatar da cewar akwai kimanin yara sama da milliyyan dari biyu da sittin da uku, a duniya da basa zuwa makaranta.

Hakan yasa suke ganin akwai bukatar samar da wannan manhajar, don a ilmantar da kowa, ya zuwa yanzu dai an samu wasu kamfanoni da zasu gudanar da aikin, yanzu haka anasa ran nan bada jimawa ba za’a fara gwajin wannan manhajar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG