Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fasaha Mai Tan-Tance Fuskar Mutun Na Kara Samun Inganci


Tun daga na’urorin zamani masu amfani da fuskar da’adam, da akanyi amfani da su a tashoshin jirage, zuwa biyan kudi a shaguna ko gidajen kalo, da wayoyin hannu, tsarin fasaha mai amfani da fuskar mutun wajen tan-tance mutun tsari ne da za’a iya amfani da shi a wurare da dama.

Kasashe kamar su China da Amurka, sun kirkiri tsarin da kuma gwada yadda tsarin zaiyi aiki, tashar jirgin sama na birnin Los Angels na daya daga cikin wurare da aka fara amfani da na’urar mai amfani da fuskar dan’adam wajen tantance fasinja, da bashi damar shiga cikin jirgi batare da yayi magana da mutun ba.

Hakan zai taimaka wajen ba mutane damar shiga jirage cikin gaggawa batare da bata lokaci wajen dube-dube da tabbatar da mutun ne ko kuma wani ne, hakan zai magance matsalar tsaro, da kuma kokarin tantance mutun da yake jikin takardun tafiya.

Kana tsarin zai taimaka wajen ganin an kama duk wani mai laifi da jami’an tsaro k enema cikin sauki, idan sabon tsarin ya samu karbuwa za’a kaddamar da shi a duk tashoshin jirage, shaguna da sauran wurare da jama’a kan taru.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG