Kasar Iran ta tsare wasu mata 35 da suka yi kokarin shiga kallon wasan kwallon kafa. Matan Sun yi kokari su je kallon wasan ne tsakanin kungiyoyin Tehran Esteqlal da Persepolis.
Iran ta ce an tsare sune na dan lokaci kuma za a sake su bayan wasan.
Shugaban Fifa, Gianni Infantino, ya halarci wasan, tare da ministan harkokin wajen Iran Masoud Soltanifar, a lokacin ne da wani dan jarida ya tambayi Ministan Soltanifar kan wani lokaci ne za a yarda mata su halarci wasan kwallon kafa a kasar ta Iran.
Sai dai Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida na kasar ta Iran Seyyed Salman Samani, ya ce ba a kama Mata magoya bayan 'yan wasan kwallon kafa ba – amma 'yan sanda sun sasu wani "wuri mai kyau".ne
Rahotannin da suka gabata sun ce mata biyu kacal aka tsare, Iran ta haramta wa mata halartar wasannin kwallon kafa tun lokacin juyin juya halin Musulunci a shekarar 1979.
Wata majiyar tana cewar kungiyar neman ‘yanci ta mata, ta bakin jagoririnta Masih Alinejad a ranar Laraba ta kira ga mata su halarci wasan da aka yi a ranar Alhamis da ta gabata.
Facebook Forum