Kamfanin Airbus, Siemens da kamfanin Rolls-Royce, masu kera motocin nishadi, na wani yunkuri na kera jirgin sama mai amfani da hasken rana. Jirgin wanda za’a yi shi dauke da farfela guda daya.
A bangare daya na jirgin za’a samar da wasu kananan injina guda uku masu amfani da mai, don gudun bacin rana, a duk lokacin da babban injin ya samu wata matsala jirgin ba zai tsaya ba.
Wannan yunkurin nasu, yayi dai-dai da zamani da ake ciki, na cigaban kimiyya da fasaha, musamman idan aka yi la’akari da yadda, ake kara samun yawaitar karuwar gurbatar yanayi a fadin duniya.
Hakan zai taimaka matuka wajen raguwar dogaro da ake yi na amfani da mai a jiragen sama, wanda hakan ke taimakawa matuka wajen gurbatar yanayi. Kamfanonin uku suka bayyana daukan alwashin kera jirgi samfurin E-Fan X, nan da zuwa shekarar 2020.
Sabon jirgin dai zai kasance yana dauke da wasu kamanni na Bae 146, wanda ke dauke da injina hudu, sabon jirgin kuwa zai dinga samar da wutar da zai rika aiki da ita da kansa a duk lokacin da yake sararrin samaniya.
Inda ita kuwa farfelar jirgin zata samar da wuta ga sauran kananan injina dake taimakama jirgin. Kamfanin kera jirage na kasashen Turai Airbus ke da alhakin kera wannan jirgin tare da sauran gudunmawa daga sauran kamfanonin.
Facebook Forum